Don haka ma Kaxaita Allah da bauta (Wato Tauhidi) shi ne tushen addini, kuma kusan kaso xaya bisa ukun Alqur'ani ya qunshi tabbatar da kaxaita Allah ne a sunayensa da siffofinsa. Kamar yadda ba a samun hutun zuciya sai ta hanyar imani da Allah mai girma da buwaya. Zuciyar da ba ta da imani za ta dauwama a cikin ruxu da rauni da rashin kwanciyar hankali. Imanin da ake samun tsira da shi, da qarfi da hutu da nutsuwa shi ne Imani da Allah mai girma da buwaya.